Barcelona ta ci Leganes 5-1

Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta koma mataki na daya a kan teburin La Liga
Barcelona ta zazzagawa sabuwar kungiyar da ta hawo gasar La Liga ta bana Leganes kwallaye 5-1 a fafatawar da suka yi a ranar Asabar.
Messi ne ya fara cin kwallo a minti na 15 da fara wasa, Sai Suarez da ya kara ta biyu daf da za a je hutu Neymar ya ci ta uku.
Minti 10 da aka dawo daga hutu Messi ya ci ta hudu kuma ta biyu da ya zura a raga, sannan Rafinha ya ci ta biyar.
Leganes ta zare kwallo daya ta hannun Appelt Pires saura minti 10 a tashi daga wasan.
Da wannan sakamakon Barcelona wadda ta yi wasanni hudu a gasar La Liga bana ta koma mataki na daya a kan teburi da maki tara.
Real Madrid wadda za ta buga wasa na hudu a ranar Lahadi da Espanyol tana matsayi na biyu da maki tara a kan teburi.