Mashaba zai san makomarsa a ranar Laraba

Kofi

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Afirka ta Kudu ba ta samu gurbin shiga gasar kofin Afirka da za a yi a 2017 ba

Hukumar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu ta ce za ta bayyana makomar kociyanta Ephraim 'Shakes' Mashaba a ranar Laraba.

Mashaba na shan suka bayan da tawagar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu ta kasa samun gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za a yi a 2017 a Gabon.

Shugaban hukumar kwallon kafar Afirka ta Kudu, Danny Jordan, ya ce a ranar Laraba ne hukumar za ta yi babban taronta, kuma a lokacin ne za ta tattauna kan makomar kociyan.

Watakila Afirka ta Kudu ta nada sabon kociya da zai zagoranci tawagar wasannin neman shiga gasar cin kofin duniya da za ta kara da Burkina Faso a Ouagadougou a Oktoba.