Wikki za ta karbi bakuncin Rivers United

Firimiya

Asalin hoton, lmcnpfl

Bayanan hoto,

Wikki tana mataki na hudu a kan teburin gasar Firimiyar Nigeria

Rivers United za ta ziyarci Wikki Tourist a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na 36 a ranar Lahadi.

Wikki tana mataki na hudu a kan teburi da maki 51, yayin da Rivers United ke matsayi na daya da maki 56.

Ga sauran wasannin mako na 36 da za a buga a ranar Lahadi:

  • Rangers da Sunshine Stars
  • Plateau United da Ikorodu United
  • Warri Wolves da Shooting Stars
  • Abia Warriors da Nasarawa United
  • Lobi Stars da Ifeanyiubah
  • Enyimba da MFM