Arsenal ta doke Hull City da ci 4-1

Premier

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Arsenal ta hada maki 10 a wasanni biyar da ta buga a gasar Premier

Hull City ta yi rashin nasara a gida a hannun Arsenal da ci 4-1 a gasar Premier wasan mako na biyar da suka fafata a ranar Asabar.

Alexis Sánchez ne ya ci wa Arsenal kwallaye biyu a karawar, inda Thio Walcott da Granit Xhaka suka ci dai-dai.

Robert Snodgrass ne ya farke wa Hull City daya a bugun fenariti, kuma kungiyar ta kammala karawar da yan wasa 10 a cikin fili bayan da aka bai wa Jake Livermore jan kati.

Da wannan sakamakon Arsenal ta hada maki 10, yayin da Hull City ke da maki bakwai a wasanni biyar-biyar da suka buga.