Crystal Palace ta ci Stoke City 4-1

Mataki

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Crystal Palace ta koma mataki na takwas a kan teburi da maki bakwai

Stoke City ta kwashi kwallaye 4-1 a gidan Crystal Palace a gasar Premier wasan mako na biyar da suka fafata a ranar Lahadi.

Tun a minti na 12 da fara wasan Palace ta ci kwallaye biyu ta hannun James Tomkins da kuma Scott Dann.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Palace ta kara cin kwallaye biyu ta hannun James McArthur da Andros Townsend.

Daf da za a tashi daga karawar Stoke City ta zare kwallo daya ta hannun Marko Arnautovic.

A wasan mako na hudu da Stoke ta karbi bakuncin Tottenham ta yi rashin nasara ne inda aka zura mata kwallaye 4-0.