Syria: MDD ta dakatadar da aikin agaji bayan hari kan ma'aikatanta

Motocin na dauke ne da kayan agaji ga mutanen da rikici ya rutsa da su

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Motocin agaji 18 ne harin ya lalata

Majalisar Dinkin Duniya ta dakatar da ayyukan agaji a kasar Syria bayan harin da aka kai wa ma'aikatanta a ranar Litinin, a birnin Aleppo.

Mai magana da yawun MDD ya ce ayarin motocin agajin sun samu cikakken izini daga dukkan masu ruwa da tsaki a yakin - ciki har da Amurka da Rasha.

An lalata 18 daga cikin manyan motoci 31, da suke dauke da alkama, da kayan sanyi, da kuma magunguna.

Wani babban jami'i na kungiyar Red Crescent ta Syria na daga cikin fararen hular da suka mutu.

Ayarin dai na dauke da ma`aikatan agaji na kungiyar Red Crescent ne `yan kasar ta Syria, wadanda ke kai kayan agaji kauyukan da ke yankin karkarar Urm al-Khubra.

Hoton bidiyon da bangaren yada labaran `yan tawaye ya fitar, wanda a ciki ake kabbara ya nuna irin rudani da aka shiga lokacin da aka kai harin.

MDD ta ce harin ya shafi akalla motoci 18 da kuma rumbun ajiyar kungiyar Red Crescent, haka kuma akwai adadin wasu ma`aikata da suka mutu ko suka jikkata.

Asalin hoton, SYRIAN CIVIL DEFENCE WHITE HELMETS/AP

Bayanan hoto,

Masu fafutuka a Syria na nuna irin barnar da harin ya yi

Wata kungiya da ke sa ido a Syria ta ce harin ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12, da kuma jikkatar wasu da dama.

MDD ta bayyana harin da cewa saba wa yarjejeniyar da aka kulla ne, kuma za ta tunkari Rasha da wannan maganar.

Amurka ta ce gwamnatin Syria da hukumomin Rasha sun san inda za a kai kayan agajin, amma duk da haka suka kai harin.

Ta ce za ta sake nazari kan hada kai da Rasha na gaba wajen cimma duk wata yarjejeniyar zaman lafiya, ko tsagaita wuta.