Nigeria: Abubuwan da 'yan majalisa za su tattauna

Kofar shiga majalisar dokokin Nigeria

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Jama'a sun zuba ido su ga wainar da za a toya a majalisar

'Yan Majalisun Nigeria sun koma aiki a karon farko bayan hutun wata biyu, inda ake sa ran za su tattauna halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Tuni rahotanni suka ce sanatocin jam'iyyar APC mai mulki sun gudanar da wani taro na sirri kan yadda za su tunkari zaman majalisar.

Hankali dai ya fi komawa ne ga majalisar wakilai sakamakon rikicin da take fama da shi da ke da nasaba da cushen ayyuka da ake zargin shugabannin majalisar da yi.

Kuma ana sa ran batun ne zai mamaye zaman na ranar Talata.

Wasu daga cikin `yan majalisar da ke karkashin kungiyar "Integrity Group" na barazanar cewa za su hana zaman majalisar har sai Kakakinta, Yakubu Dogara ya sauka daga mukaminsa.

Sai dai Kakikin majalisar Abdurrazaq Namdas, ya shaida wa BBC cewa batun halin da tattalin arzikin kasar ke ciki ne za su mayar da hankali a kai.

Sannan ya kara da cewa duk wanda ya ke son wani ya sauka daga mukaminsa, to sai ya gabatar da kuduri domin neman rinjaye, kamar yadda doka ta tanada.

Bayanan sauti

Me 'yan majalisun Nigeria za su tattauna