Jam'iyyar Angela Markel ta sha kasa a zaben birnin Berlin

Wannan ne karon farko da CDU ta fadi a Berlin
Bayanan hoto,

Jam'iyyar CDU ta Angela Markel ta sha kasa a Berlin

Jam`iyyar Christian Democrats ta shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel ta yi mummunar faduwa a zaben jihohi, wadda ba ta taba yin irin ta ba a Berlin.

Kuri`un da jam`iyyar ta samu ba su kai kashi 18 bisa dari ba, lamarin da ya tilasta mata fita daga gwamnatin jiha ta hadin-gwiwa.

Da alama hukuncin da Angela Merkel ta dauka na kyale masu 'yan gudun hijira kimanin miliyan daya a bara, shi ne ya janyowa jam'iyyar ta ta wannan mummunan kaye.

Jam'iyyar masu tsaurin ra'ayi da ke kyamar baki AFD ita ce ta fi cin moriyar sakamakon zaben.

A yanzu jam'iyyar ta AFD za ta samu wakilci a majalisun gundumomi goma, ciki har da Berlin.

Jam'iyyar dai tana fatan samun irin wannan nasara a zaben gama gari da za a yi badi, inda take fatan kawo karshen kawancen da aka jima ana yi tsakanin jam'iyyar CDU ta Angela Merkel da kuma jam'iyyar Social Democrats.