MDD na taro domin warware matsalar 'yan gudun hijira

MDD na babban taro kan 'yan gudun hijira

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Wannan ne babban taron MDD na farko kan 'yan gudun hijira

Majalisar Dinkin Duniya za ta gudanar da taronta na farko a birnin New York kan 'yan gudun hijira da 'yan ci rani, da nufin samar da wani yanayi da kasashen duniya za su dunkule wajen samar da tallafi bai daya.

Babu wani batu da ke kara raba kan duniya a siysance sama da makomar mutane miliyan 21 dake gujewa tashin hankali da cuzgunawa a duka fadin duniya, da kuma kaura da mutane masu dimbin yawa ke yi don neman ingantacciyar rayuwa.

MDD na son a tattauna a kan batutuwan a taron na ranar Litinin din nan, hakan ta sa majalisar ta kira shi 'wata muhimmiyar dama ta tarihi da za ta zo da wani tsari mafi nuna dattako da ake fatan aiwatarwa, wanda kuma zai yi daidai da bukatun 'yan ci rani da 'yan gudun hijira.

To sai dai gwamnatoci suna da ra'ayoyi mabanbanta, kuma da damansu sun ki amincewa da tsarin daukar nauyin 'yan gudun hijirar tare, sabo da sanin yadda ake kyamatar 'yan ci rani a kasashensu.

Kungiyar Amnesty International ta ce taron zai zama taron tsinitsiya ba sahara ne, sabo da daftarin da za a futar a karshen taron bai kunshi alkawuran da kasashe za su yi ba na karbar masu neman mafaka.

Kuma bisa haka ne shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta MDD Filippo Grandi ya shedawa BBC cewa ya kamata kasashen duniya su hada hannu domin magance matsalar da ta zamewa duniya alakakai.

Yace "idan kasashe a nahiyar turai suka yi aiki, za su magance wannan matsalar, amma ba wai su ringa aiki a daidaikunsu ba, kamar yadda lamarin ya ke yanzu."

Yace abu ne mai muhimmanci a saurari wadanda ke adawa da kwararar dubban 'yan gudun hijira, to amma ya caccaki 'yan siyasa da ke kyamatar baki, abinda yace ana tsorata su ne kawai da labaran kanzon kurege.