Koriya ta Arewa ta yi sabon gwaji injin harba 'Roka'

Koriya ta yi harin ne duk da adawar da duniya ke nuna mata

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un ne ya sa ido a lokacin gwajin

Koriya ta Arewa ta ce ta samu nasarar gwajin wani inji mai harba roka.

Kamfanin dillancin labaran kasar ya rawaito cewa sabon injin zai taimaka wa Koriya wajen harba tauraran dan`adam iri daban-daban cikin sararin samaniya.

Shugaban kasar Kim Jong-Un ne ya sa-ido wajen yin gwajin.

A farkon wannan watan ne Koriya ta Arewar ta bijire wa takunkumin Majalisar Dinkin Duniya, inda ta jarraba wasu makamai masu linzami.

Ana dai zargin cewa kasar na fakewa da wannan shiri na harba tauraran dan`adam din ne domin ta bunkasa shirinta na kera makami mai linzami mai cin dogon-zango.

Kuma Kakakin hafsoshin sojin Koriya ta Kudu Jeon Ha-kyu ya ce suna nan suan sa ido.

Ya ce "bisa la`akari da sanarwar da Koriya ta Arewa ta yi, muna jin cewa injinsu ya kara inganci. Za mu sa ido a kan zirga-zirgar sojojinsu a watan gobe".