Hukumar Halcia ta gano malaman makaranta na bogi 2000 a kasar Niger

An gano malaman makaranta na bogi 2000 a Niger

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Gwamnati Niger na cigaba da bincike domin gano malaman makaranta na bogi a kasar

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa HALCIA a Jamhuriyar Niger, ta ce ta gano malaman makaranta yan kwantaragi sama da dubu 2 na bogi.

Hukumar dai ta gano malaman ne a cikin jihohi 5 daga cikin 8 da kasar ke da su.

Gwamnatin kasar dai na yin asarar biliyoyin cefa a kowace shekara sakamakon biyan wadannan malamai.

Hukumar dai ta tabbatar da hakan ne a lokacin da ta gudanar da wani bincike da ta yi a kasar.

Sai dai kungiyar malaman makarantar 'yan kwantaragi, ta ce ba ta yi farin ciki da jin sakamakon binciken da hukumar HALCIA ta yi ba.

Amma kungiyar ta kara da cewa akwai bukatar hukumar ta cigaba da binciken domin tantance masu hannu a cikin badakalar.