Faransa: Za a saka kamarori a mayanka

Kwamitin bincike na majalisar dokokin Faransa ta na so a saka kamara a mayanka

Asalin hoton, L214

Bayanan hoto,

Kungiyoin kare hakkin dabbobi sun koka kan lamarin

Wani kwamitin bincike na majalisar dokokin Faransa ya bayar da shawarar a saka kamara a mayanka domin kauce wa cin zarafin dabbobi.

Kwamitin ya kuma nemi a bullo da wata hanya wadda al'ummar Musulmi da Yahudawa za su yarda da ita wadda za a bi wajen fitar da dabbobin daga hayyacinsu kafin a yanka su.

Kungiyar rajin kare hakkin dabbobi ta L214 ta fitar da bidiyon wani rago a cikin wani mawuyacin hali a lokacin da ake yanka shi a daya daga jikin manyan abbatuwa da ke kasar.

A cikin bidiyon har da dabbobin da aka rataye a wani karfe suna shure-shuren mutuwa bayan an yanka su da hannu.