An gayyaci 'yan wasa 30 tawagar kwallon kafa ta mata

Asalin hoton, The NFF
Nigeria tana rukunin da ya kunshi Japan da Canada da kuma Spaniya
Kociyan tawagar kwallon kafa ta mata ta Nigeria, Peter Dedevbo, ya gayyaci 'yan wasa 30, domin shirin tunkarar gasar kofin duniya ta matasa 'yan kasa da shekara 20.
Tuni kociyan ya umarci 'yan wasan da aka gayyata da su isa otal din Serob Legacy da ke Abuja a ranar Talata 27 ga watan Satumba tare da takardun haihuwa da kuma fasfo din su.
Nigeria tana rukunin da ya kunshi Japan da Canada da kuma Spaniya
Za a yi gasar matasa ta mata 'yan kasa da shekara 20 a Papua New Guinea daga ranar 13 ga watan Nuwamba zuwa 3 ga watan Disamba.