Sojoji sun ƙwace Malam Fatori daga hannun Boko Haram

Garin Malam Fatori yana da muhimmanci ga Najeriya da Nijar
Bayanan hoto,

An kashe 'yan Boko Haram da dama yayin musayar wuta.

Rundunar sojan Najeriya ta ce dakarunta tare da na rundunar tsaro ta hadin gwiwa a yankin tafkin Chadi sun kwato garin Malam Fatori a arewacin jihar Borno daga hannun mayaƙan Boko Haram.

Wata sanarwa da mukaddashin jami'in hulda da jama'a na rundunar sojan Najeriya, Kanar Sani Usman Kukasheka, ya fitar ta ce an yi amfani da sojojin kasa da kuma jiragen yaki wajen fatattakar 'yan Boko Haram daga garin, wandanda da farko suka tilastawa sojojin ja da baya.

Kukasheka ya shaida wa BBC cewa 'yan Boko Haram din sun kai wa sojojin rundunar tsaron hadin gwiwa hari a garin, wanda yake kan iyakar Najeriya da Nijar.

Ya ce sojojin sun fatattake su, sannan jiragen yaƙi su ka kai dauƙi, inda aka kashe 'yan Boko Haram din da dama.

Kanar Usman bai bayyana adadin 'yan Boko Haram din da aka kashe ba, kuma ya ce babu ko da soja daya da aka jikkata ko ya rasa ransa.

Malam Fatori dai shi ne gari mafi girma a karamar hukumar Abadam da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya, kuma dubban 'yan gudun hijira na samun mafaka a garin.