Amnesty ta zargi 'yan sandan Nigeria da azabtar da mutane

'Yan sandan ba su ce komai ba kan rahoton
Bayanan hoto,

Amnesty ta ce 'yan Sandan Nigeria na gallazawa jama'a

Kungiyar kare hakkin bil`adama ta Amnesty International ta zargi rundunar `yan sandan Najeriya da ke yaki da `yan fashi da wuce gona-da-iri wajen azabtar da jama`a, tare da karbar rashawa.

Wani rahoton da kungiyar ta futar a ranar Larabar nan, bayan tattara bayanai daga mutanen da suka taba shiga hannun rundunar `yan sandan, ya ce `yan sandan suna gallaza wa jama`a azaba, inda wuya kan sanya su amincewa da aikata laifi, yayin da wani lokaci suke ba da cin hanci domin su samu sa`ida.

Wani sashi na musamman na rundunar 'yan sandan wanda aka fi sani da Sashin masu yaki da 'yan fashi ko kuma SARS, ya yi kaurin suna a Nigeria wajen ganawa mutane azaba a cewar kungiyar ta Amnesty International.

Kungiyar mai kare hakkin dan adam ta ce mutanen da aka taba tsarewa a wajen, sun bata bayanin irin gwale-gwalen da ake yiwa duk wanda aka kai wajen, da suka hada da ratayewa, da horon yunwa, da harbi, da kuma barazanar kisa.

Kungiyar ta yi zargin cewa a yanzu sashin ya koma na azabtar da mutane, da cin hanci da rashawa, maimakon kare su wanda shi ne manufar kirkirar sashin.

Rahoton ya ce rundunar `yan sanda na da gadirun da dama a kewayen Abuja, babban birnin kasar, inda take tsare mutane, ciki har wani wuri da aka lakaba masa suna "kwata" ko "mayanka," inda Amnesty ta yi zargin cewa ana tsare da mutane 130 a cikin halin matsi.

Rundunar `yan sandan Najeriyar dai ba ta ce komai ba dangane da wannan zargin.