Majalisa dinkin duniya za ta shawo kan cututtuka masu bijirewa magunguna

Ana ci gaba da taron kasashe mambobin MDD a New York

Asalin hoton, AP

Bayanan hoto,

MDD za ta shawo kan cututtuka masu bijirewa magunguna

A ranar Laraba ne dai ake sa ran duka kasashe mambobin Majalisar Dinkin Duniya za su rattaba hannu a kan alwashin da suka yi na yaki da cututtuka masu bijire wa magunguna.

Wannan alkawarin dai wata manuniya ce cewa duniya ta dauki cututtuka masu bijire wa magani a matsayin wata babbar barazana ga harkar kiwon lafiya a duniya.

Wuce kima wajen amfani da magunguna masu kashe kwayoyin cuta na daga cikin abubuwan da ke haddasa matsalar bijirewar da cututtuka ke yi ga magunguna.

Majalisar Dinkin Duniya muddin ba a samar da wasu sabbin magunguna ba, to, da wuya a gudanar da wasu ayyukan jinya da suka hada da tiyatar haihuwa da sauya katare.

Akalla mutum 700, 000 ke mutuwar a duniya a kowace shekara, sakamakon bijirewar da cututtuka ke yi wa magunguna.