Chibok: Buhari na son MDD ta shiga domin tattaunawa

Bidiyon 'yan matan Chibok
Bayanan hoto,

Daya daga cikin 'yan matan Chibok a bidiyon Boko Haram na baya-bayan nan

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya gayyaci Majalisar Dinkin Duniya ta shiga tsakanin domin a tattauna da kungiyar Boko Haram a yi musayar 'yan matan Chibok.

Buhari ya yi wannan kira ne yayin da ya gana da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban-Ki- Moon, a wajen taron majalisar da ke gudana a Amurka.

Shugaban na Najeriya ya ce gwamnatinsa a shirye take ta tattauna da 'yan Boko Haram kan sako 'yan matan, to amma tana so ta san su waye shugabannin kungiyar na hakika.

Ya ce gwamnatin Najeriya na son tattaunawa, amma rikicin shugabancin da kungiyar ta Boko Haram ke fama da shi ya kara kawo tsaiko a yunkurin ceto 'yan matan na Chibok.

Buhari ya ce gwamnatinsa na maraba da shigar kungiyoyi ko hukumomi na duniya masu mutunci domin a tattauna yadda za a sako 'yan matan.

To amma fa shugaban ya kuma caccaki Boko Haram da cewar hare-haren da take kai wa sun saba da koyarwar addinin musulunci.

Wata sanarwa da mai bai wa shugaba Buhari shawara kan hulda da jama'a Femi Adesina ya fitar ta ce Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban-ki-Moon ya yaba wa Buhari kan nasarar da aka samu a yaki da Boko Haram, kodayake ya gargade shi da a ringa kiyaye hakkin bil-adama.