Zuckerberg ya ware $3bn domin yaki da cutuka

Mark Zuckerberg da iyalinsa Priscilla Chan

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mark Zuckerberg da matarsa Priscilla Chan

Mai kamfanin shafin sada zumunta na Facebook, Mark Zuckerberg da iyalinsa Priscilla Chan, sun yi alkawarin taimakawa da dala biliyan uku don gudanar da binciken kimiyya da nufin yaki da cututtuka a duniya, a cikin shekaru goma masu zuwa.

Manufar agajin dai ita ce samar da magani da alluran riga-kafin cututtuka.

Tallafin zai hada da dala miliyan 600 da za a kashe wajen bincike a wata cibiya a California.

Sun dai sha alwashin cewa za su yi amfani da arzikinsu wajen kyautata rayuwar duniya domin `ya`yansu su ji dadin wanzuwa a ciki.

Mark Zuckerberg ya ce "wannan ba ya nufin cewa babu wanda zai harbu da cuta, ma`ana ita ce masu rashin lafiya za su ragu, kuma za a yi musu jinya cikin gaggawa".