Za ka iya aikin da zai kai ka ga mutuwa ?

Mutuwa saboda yawan aiki ba sabon abu ba ne a Japan
Bayanan hoto,

Mutuwa saboda yawan aiki ba sabon abu ba ne a Japan, domin har akwai wata kalma da su ke kiran irin wannan mutuwa. Shin hakan kuwa zai taba yiwuwa?

Al'ummar Japan sun shahara wajen ƙirkiro kalmomi - akwai ma wasu kalmomin da kowane ma'aikaci mai mutunci ya kamata ya riƙa amfani da su yau da kullum.

Akwai kalmomi kamar su arigata-meiwaku: wanda ke nufin idan mutum ya yi maka alfarma da ba ka tambaye shi ba a wani lamari da ya dame ka amma kuma ya zama maka wajibi ka yi masa godiya.

Akwai kuma kalmar majime: abokin aiki mai ƙwazo wanda zai yi wani abu tare da an ji ku ba.

Daga shekarar 2015 an samu ƙaruwar iƙirarin da ake yi na mutuwar mutane saboda yawan aiki inda ya ƙaru zuwa 2,310 sai dai akwai wata kalma a harshen Japan da mutum ba zai taba so ya yi amfani da ita ba: karoshi, kalmar da ke nufin "mutuwa saboda yawan aiki".

Rahotanni mutuwar ma'aikaci wanda shi ne ke daukar nauyin iyalan sa sun sha mamaye kanun labarai na jaridun kasar a shekaru masu yawa.

Bayanan hoto,

Mutuwa saboda yawan aiki wata matsala ce a Japan - wasu sun ƙiyasta cewa adadin mutanen dake mutuwa sun zarta 10,000

An dai fara gano wannan matsala ce tun daga shekarar 1987 lokacin da ma'aikatar lafiya ta fara tantance adadin mutanen da ke mutuwa farad daya wadanda galibin su manyan ma'aikata ne.

Bayan rashin nasara a yakin duniya na 2 'yan kasar Japan su suka fi kowace al'umma yawan sa'ao'i na aiki a duniya in ji - Cary Cooper

Har ta kai ga yadda wannan matsala ta yadu a Japan da zarar aka tabbatar mutuwar karoshi ce, gwamanti na biyan diyya ga iyalan mamacin na kusan dala dubu ashirin a duk shekara yayin da kamfanoni kan biya kusa dala miliyan daya da dubu dari shida.

Tun da farko dai gwamnati tana kididdige yawan daruruwan mutanen dake mutuwa a kowace shekara, amma daga 2015 adadin ya ƙaru zuwa dubu 2,310, a cewar wani rahoto da ma'aikatar ƙwadago ta ƙasar ta fitar.

Wannan dai somin tabi ne a cewar hukumar dake kare hakkin iyalai na wadanda suka yi mutuwar karoshi, domin adadin zai zarta 10,000 - wannan shine yawan mutanen dake mutuwa sakamakon hadurran ababen hawa a kasar a kowace shekara.

Bayanan hoto,

Ba wai Japan ba kadai - kasashen da suka ci gaba da dama na fuskantar irin wannan matsala.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

Amma tambayar anan ita ce, ko mutum zai iya mutuwa saboda yawan aiki? Ko dai saboda tsufa ne ko kuma rashin lafiyar da ba'a kaiga gano ta ba?

Wannan dai wani abu ne dake da alaka da yanayin da ake ciki a duniya inda fasahar zamani ta mamaye mu a cikin sa'o'i 24 na kowace rana, aiki na shigo mana akai akai.

Mutuwa saboda yawan aiki

Wani misali na mutuwar karoshi shi ne na Kenji Hamada wanda aka dauke shi aiki a matsayin mai gadi a wani kamfani dake Tokyo kuma yana bin ka'idojin aiki sau da kafa.

Yanayin aikin sa shine sa'o'i 15- a kowace rana da kuma sa'o'i 4 da yake shafewa akan hanyar sa ta zuwa da komawa gida.

Wata rana kwatsam sai aka ga ya bingire a akan tebur, inda abokan aikin sa suka zaci cewa yana barci ne.

Da suka ga ya shafe sa'o'i bai motsa ba a lokacin ne suka gano cewa ya mutu.

Ya mutu ne sakamakon bugun zuciya yana mai shekaru 42.

Koda yake Hamada ya mutu ne a shekarar 2009, amma mutuwar karoshi ta faro ne shekaru 40 da suka gabata lokacin da wani matashi mai shekaru 29 ya samu shanyewar bangaren jikin sa bayan ya kammala wani aiki na horo a sashen rarraba jaridu a babban kamfanin jaridar kasar.

A lokacin da tattalin arzikin kasar ya ke habbaka, kusan mutane miliyan bakwai ne ke aikin sa'o'i 60 a kowane mako.

Cary Cooper wani masani a harkar ayyukan dake haddasa cututttuka a jami'ar Lancaster ya ce tun bayan rashin nasarar da Japan ta samu a yakin duniya na 2 , 'yan kasar su suka fi kowane al'umma a duniya yawan sa'o'i na aiki.

Shekaru da dama a tsakiyar 1980 lamarin sai ya sauya.

Al'amura sai suka daina tafiya yadda ya kamata a kasar ta fuskar tattalin arziki tare da hauhawan farashin hannayen jari da kuma gidaje, hakan ya sa tura ta kai bango ga ma'aikata a Japan.

Bayanan hoto,

Dillalai a tsakiyar zauren kasuwar hannayen jari a Tokyo a watan Maris na 1992

A lokacin da tattalin arzikin kasa ya ke habbaka, kusan mutane miliyan bakwai ne wadanda suka kai kashi 5 cikin 100 na ma'aikatan kasar a lokacin suke aikin sa'o'i 60 a kowane mako.

A halin yanzu kasashen Amurka da Burtaniya da Jamus su ma suna neman bin irin wannan sahu na yawan lokaci ana aiki.

A shekarar 1989, kashi 45.8 cikin 100 na manyan shugabanni da kuma kashi 66.1 na matsakaitan shugabanni a kamfanoni sun zaci cewa su kansu zasu iya mutuwa saboda yawan aiki.

Daga ƙarshen shekarar 1980 ma'aikata dake samun albashi mai tsoka suna mutuwa a duk shekara saboda yawan aiki har sai da ta kai ga gwamnati ta fara sa ido sosai.

Mutuwar karoshi ta zama abun damuwa ga ma'aikatar kwadago ta kasar inda ta fara wallafa sunayen mutanen dake mutuwa.

Mutuwar ma'aikaci a yayin da bai tsufa ba saboda cututtuka kamar ciwon zuciya da ciwon suga wani abu ne guda.

Amma mutuwar matashi a lokacin da yake tashe kamar likitoci, malaman jami'o'i da injiniyoyi sun ci gaba da haddasa damuwa.

Bayanan hoto,

Gajiya tana haddasa wasu dabi'u kamar shaye shaye da shan sigari wanda kan sa mutum ya mutu da wuri.

Ko yawan aiki na da illa?

Daga cikin dubban misalai na irin wannan mutuwa, akwai wasu abubuwa guda biyu da su ke kan gaba- Gajiya da kuma rashin barci.

Ko wadannan za su iya haddasa mutuwa?

Kuma menene yawan sa'o'in daya kamata ma'aikaci ya yi a wurin aiki kafin ya shiga matsala?

Zuwa aiki bayan ka shafe dare kana wasu abubuwa zai iya sa ka fita cikin hayyacin ka.

Amma kuma abun mamaki hujjojin da ke nuna cewa rashin barci zai iya hallaka mutum ba su da yawa.

Kundin al'ajabi na duniya wato Guinness World Record da ya nuna tsawon lokacin da mutum ya shafe ba tare runtsa ido ba shine wanda Randy Gardner ya yi na tsawon sa'o'i 264 (wato kwanaki 11 idon sa biyu) a shekarar 1964.

A ranar ta karshe, ya laharci wani taron manema labaru inda daga bisani ya kwashe sa'o'i 14 da minti 40 yana ta barci.

Kuma yanzu haka yana nan da ransa a San Diego.

Bayanan hoto,

Rashin barci kan haddasa cututtuka masu tsanani

Kuma sabanin yadda ake zato babu wata shaida data nuna cewa gajiya kadai tana haddasa ciwon zuciya ko kuma haddasa bugun zuciya.

Koda yake zai iya haddasa wasu munanan dabi'u kamar shan taba sigari da shaye shaye.

Amma me zai faru idan aka hada da mutuwar da ake yi sakamakon cututtuka kamar cutar kansa ?

An yi amannar cewa gajiya tana da illa, amma a bara wasu kwararrun masana kimiyya daga jami'ar Oxford sun yi nazari akan batun.

Sakamakon bincikensu ya nuna cewa mata wadanda suke fama da gajiya kuma basa farin ciki sun fi hadarin mutuwa da sauri.

Kamar yadda ake zato, rahotannin mutuwar karoshi a wajen kasar Japan na karuwa.

Kasar Sin ta yi asarar mutane dubu 600,000 saboda guolaosi - kamar yadda ake kiran irin wannan mutuwa a kasar - a duk shekara kimanin mutane 1,600 kenan a kowace rana.

Bayanan hoto,

Bara, an samu karuwar mutuwar karoshi a Japan

"Kasashen India, da Koriya ta Kudu da Taiwan da kuma China - kasashen da su ne masu karfin tattalin arziki masu tasowa na neman bin sahun Japan- in ji Richard Wokutch wanda ya wallafa littafi akan hadarin da ake samu a wuraren aiki.

"Ya ce ba mun taba samu irin wannan lamari a birnin London ba? Amma shiru ka ke ji in ji Cooper.

Kuma yana da gaskiya domin a watan Ogustan shekarar 2013, wani ma'aikacin wucin gadi a bankin Amurka Merrill Lynch, Moritz Erhardt an ga gawar sa a lokacin da yake wanka bayan da ya shafe sa'o'i 72 a jere yana aiki ba hutawa.

An dai gano cewa matashin mai shekaru 21 ya mutu ne sanadiyar cutar farfadiya, kuma bayan mutuwar sa sai bankin ya takaita yawan lokacin aiki zuwa sa'o'i 17.

Bayanan hoto,

Rashin barci dai kan haddasa kamuwa da cututtuka - koda yake babu wanda aka ce ya taba mutuwa saboda ya hana idonsa barci haka kaiwa

A kasar Japan, kananan ma'aikata basa jin dadi su ta shi daga aiki kafin lokacin tashin shugabannin su.

Domin a lokacin da nake aiki a can, mutane da dama kan dauko jaridu bayan sun tashi aiki.

Ba za su tafi gida ba amma kuma zaka ga suna aiki, suna duba shafukan sada zumunta ko kuma karance karance.

Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilishi latsa nan: is there such thing as death from overwork