Ka san irin aikin da ya fi dacewa da ragon mutum?

Ko kuma abun daya fi dacewa da tsarin rayuwar aiki shine na bin hanyar da ba'a bukatar sadaukarwa da yawa?
Bayanan hoto,

Ko kuma abun daya fi dacewa da tsarin rayuwar aiki shine na bin hanyar da ba'a bukatar sadaukarwa da yawa?

A yanayin da tsananin gajiya saboda aiki ke ƙaruwa, shin ko neman aikin da ba shi da wahala wanda ake biyan albashin mai tsoka shi yafi dacewa da mutum mai tsananin basira?

Ko kuma abun daya fi dacewa da tsarin rayuwar aiki shine na bin hanyar da ba'a bukatar sadaukarwa da yawa?

Shin menene aibun neman aikin da bai da wahala sosai ne?

Mun nemi jin amsar wadannan tambayoyi a shafin internet na Quora don neman shawarwari akan aikin daya fi dacewa da mutanen da ke da ƙwazo da kuma ragwaye. Ga abun da wasu talakawa ke cewa:

Turanci ga kowa?

Mai tsara manhajar wasannin a na'urar kwamfuta, Andy Lee Chaisiri ya rubuta cewa: 'Mai yiwuwa malami daya cikin malamai uku dake koyar da darussan turanci da muka hadu a Beijing na bayyana kansa a matsayin mutum mai basira, amma kuma babban rago.'

Ya ƙara da cewa aikin koyarwa a ƙasar Sin aiki ne da ake samun albashi mai tsoka wanda kuma ake matukar neman sa amma kuma ba'a takaita ƙa'idar shiga aikin koyarwa ba.

Skip Podcast and continue reading
Podcast
Korona: Ina Mafita?

Shiri na musamman da sashen Hausa na BBC zai dinga kawo muku kan cutar Coronavirus

Kashi-kashi

End of Podcast

A wasu lokuta abun da kawai ake bukata ga mai neman aikin shine ya kasance an haife shi a ƙasar da turanci ne harshen al'ummar kasar.

Chaisiri ya kuma bayyana cewa saboba koyar da turanci yana da sauƙi ta fuskar sa'o'in aiki, mutane da dama dake koyar da turanci na yi ne a matsayin wucin gadi- suna yi ne domin taimakawa iliminsu ko kuma hutu na wani taƙaitaccen lokaci ko kuma su nemi wani aiki, wanda hakan ke nufin idan ka yanke shawarar cewa koyar da turanci shine sa'anar ka, zaka riƙa samun ci gaba akai-akai.

Ya ƙara da cewa: "idan kudin da kake samu zai yi daidai da matsakaicin matakin dalibi wanda ya kammala kwaleji kuma yake aiki na sa'o'i 50 a kowane mako, kuma yana ƙara lokacin aiki har sai rayuwarsa ta kare, a don haka Chaisiri ya ce: "Sai ka je ka koyar da turanci, a matsayinka na ragon mutum!"

Na'urar rubutu na kwamfuta da rigunan barci

Idan baka damu ba koda wurin aikinka ya kasance nesa da gida, Paul Denlinger ya bada shawarar cewa: "Mai tsara mahanjar kwamfuta: wannan wani aiki ne da ake ci gaba da samun ƙarin ilimi akai-akai, amma ba sai mutum ya ƙara himma ba, saboda sannu a hankali zaka fahimci cewa akasarin ƙalubalen da ake fuskanta maimaici ne."

Ya ƙara da cewa, koda kuwa irin yanayin aikinka ya kasance irin wanda bai zama tilas a gareka ka ba ƙara himma "mutanen da suka ƙware a harkar tsara manhajar kwamfuta su kan rubuta wasu kalmomi ƙalilan ta yadda zasu fahimta, kuma wannan na daga cikin irin ayyukan da ake samun albashi mai tsoka, yayin da a bangare guda kuma yake ƙara ƙwarin gwiwar mutum ya zama rago.

Denlinger ya ce. "Har ila yau a lokaci guda kuma za ka je aiki da wasu mutane masu kaifin basira da suke da ilimi na musamman yayin da masu zuba jari ke biyanka kudade akan wasu tunani da zasu bullo da su anan gaba.

Sai dai Chris Leong wani ƙwararre a harkar tsara mahajar kwamfuta dake Sydney ya kawo shawarar cewa "yin aiki da gwamnati, akasarin masu ayyukan na samun sa'o'i 35 ne cikin makwanni a Australia — sai dai idan mutum ya kasance babban ma'aikaci ne".

Tambaye ni, ni ƙwararre ne

Matthew Kuzma ya rubuta cewa "Ra'ayi na shine aikin daya fi dacewa ga mutumin dake da basira amma kuma rago shine ya zaman ƙwararre a wani fanni yadda idan za'a riƙa biyansa domin ya bayyana tunaninsa da shawarwarin sa game da wasu abubuwa ga mutanen da zasu aiwatar da su."

Ya kuma kawo shawara ga masu zaman banza akan su "gano ayyukan da suke ganin ba ayyuka ba ne kuma su nemi aikin da za'a riƙa biyan su, domin akwai yiwuwar cewa abubuwan da suke ganin abun dariya ne ga wani mutum, abubuwa ne masu wahala ga wasu kuma a shirye suke su biya ka domin ka yi musu irin wadannan ayyukan."

Ko wani lokaci akwai mafita

Kamar dai yadda ya faru ja da baya ga wasu ayyukan ba kowane lokaci ne yake kasancewa bai shi da kyau ba Arvind Krishnan ya ambato attajirin nan Bill Gates na cewa "Zan zabi mutum rago ya yi min aikin daya fi wahala saboda zai samun hanyar data fi sauki domin yin aikin."

A don haka ina mutane ragwaye a duniya :"Da alama kuna da abun yi a Microsoft," in ji Krishnan.

Idan kana son karanta wannan labarin a harshen Ingilishi latsa nan: Jobs for the smart but lazy