'Yan sanda a Sierra Leone sun sako matar da aka kama da yin kaciyar mata

An sako wadda aka zarga da kaciya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

'Yan sanda a Sierra Leone sun sako matar da aka kama da yin kaciyar mata

'Yan sanda a kasar Saliyo sun sako wata mata wadda ake zargi da yin kaciyar mata bayan matsin lamba daga wata kungiyar masu yin kaciya.

'Yan sanda a kasar Saliyo sun saki wata mata da ake zargi da yi wa mata kaciya bayan da wata kungiyar masu yin kaciya mai karfin fada-a-ji ta matsa lamba.

Sufeton 'yan sanda a Saliyon ya ce an sako Elsie Kondoromoh bayan da wadansu masu aikin yanka karafuna da dama

suka yi zanga-zangar kin amincewa da kama ta da 'yan sanda suka yi.

Sun kuma yi wata zanga-zangar a wani asibiti inda ake zargin wacce ta yi wa kaciyar na samun kulawa.

A halin da ake ciki yanzu, an hana kaciyar mata a kasar Saliyon.

An dai tsaurara matakan hana kaciyar ne bayan barkewar cutar Ebola a watan Disamba na shekarar 2013, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane 11,000.

Mabiya addinin gargajiya, wadanda suke kallon kaciyar mata a matsayin wani munzali na cika mace ga yara mata, sun dawo da ita a wantannin baya-bayan nan.

Sai dai kuma masu fafutuka da dama suna dora alhaki a kan gazawar da hukumomi suka yi wajen hana kaciyar saboda karfin fada-a-ji na masu kaciyar.