Nigeria: 'Yar shekara 25 za ta shugabanci karamar hukuma

Hajiya Hindatu Umar, sabuwar shugabar karamar hukumar Argungu
Bayanan hoto,

Wadansu na ganin Hajiya Hindatu Umar ba ta da kwarewar da ta dace

Wata matashiya 'yar shekara 25 ta zama sabuwar shugabar karamar hukumar Argungu dake Jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya.

Ranar Alhamis da yamma ne dai Hindatu Umar ta dare kujerar shugaban karamar hukumar, wacce daya ce daga cikin kananan hukumomin da ke da muhimmanci a Jihar.

Rahotanni sun ce Malama Hindatu ta zama shugabar karamar hukuma ne bisa umarnin gwamnatin Jihar cewa ta maye gurbin tsohon shugaban wanda wa'adin mulkinsa, da na sauran shugabannin kananan hukumomin Jihar, ya kare a makon jiya.

An ce kafin karewar wa'adin ita ce mataimakiyar shugaban.

Sai dai kuma jama'a da dama a karamar hukumar da ma sauran sassan jihar na sukar wannan mataki saboda a cewarsu ita ma ya kamata a ce ta sauka tare da shugaban tun da tare aka nada su.