Majalisar kolin Nigeria ta ki amincewa a sayar da kadarorin gwamnati

Gwamnonin jihohin Najeriya 36 na cikin Majalisar Kolin
Majalisar koli kan tattalin arzikin Najeriya ta ce ba ta goyi bayan kiraye-kirayen da wasu suka yi ba na a sayar da wasu kadarorin kasar domin magance matsalar tabarbarewar tattalin arzikin da kasar ta samu.
A ranar Laraba ne dai shugaban majalisar dattawan kasar, Sanata Bukola Saraki da hamshakin dan kasuwar nan Aliko Dangote suka yi kira da a sayar da kadarorin kasar.
Kadarorin da ake magana a kai sun hada kamfanin sarrafa iskar gas na NLNG da kamafanin mai na kasar NNPC da dai sauran su.
Sai dai a zaman da Majalisar koli kan tattalin arzikin Najeriya ta yi na ranar Alhamis, ta ce ba ta goyi bayan kiran ba.
Amma kuma Majalisar ta ce ta goyi bayan shirin gwamnatin tarayya na farfado da tattalin arzikin kasar.
Majalisar, wadda ta kunshi gwamnonin jihohin kasar, ta kuma yi watsi da kiraye-kirayen da wasu 'yan majalisar dattawan kasar suka yi na a cire ministocin kudi da na kasafin kudu da tsare-tsare.
'Yan majalisar dattawan Najeriya dai sun yi kira a sauya ministocin bisa zargin gazawa wajen farfado da tattalin arzikin kasar.