Facebook ya zuzuta kiyasin yawan bidiyon da mutane suka kalla

Wani ma'abocin Facebook yana duba shafinsa

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Facebook ya yi watsi da faya-fayan bidiyon da tsawonsu bai kai sakan uku ba

Kamfanin Facebook ya zuzuta hasashen da ya yi na yawan mutanen da suka kalli bidiyo a shafinsu a shekaru biyu da suka wuce.

Wani mai talla ya ce a wadansu lokutan, ana zuzuta kiyasin yawan kallon bidiyo da aka yi har zuwa kashi 80 cikin 100.

Kiyasin da Facebook ke yi na yawan mutanen da suka kalli bidiyo na da muhimmanci a wajen masu talla a shafin.

Masu tallar suna amfani da kiyasin wajen gane yawan mutanen da suka kalli bidiyon da suka wallafa a shafin Facebook din.

Kamfanin Facebook ya ce an gyara kuskuren da aka yi kuma hakan bai sauya kudin da masu talla suke biya domin yin amfani da shafin ba.