Donald Trump zan zaɓa — Ted Cruz

Ted Cruz ya ce zai zabi Trump saboda tsare-tsarensa

Asalin hoton, Spencer Platt

Bayanan hoto,

Donald Trump ne dan takarar jam'iyyar Republican

Mutumin da aka kayar a zaben cikin gida na shugabancin Amurka a jam'iyyar Republican, Ted Cruz, ya mara wa Donald Trump baya, a takarar shugabancin Amurka.

Ted Cruz dai ya yi hamayya sosai da Donald Trump, kafin zaɓen cikin gidan jam'iyyar.

Shi dai Mista Cruz wanda Sanata ne mai wakiltar jihar Texas, ya bayyana goyon bayan nasa a shafinsa na Facebook.

Sanatan ya ce ya yanke shawarar ya mara wa tsohon abokin hamayyarsa baya saboda wasu tsare-tsare guda shida da suka hada da batun makamashi da 'yan ci-rani.