Mutum 2m na fama da matsanancin rashin ruwa a Aleppo

Kishirwa na neman kashe mutum 2m

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mutane na fuskantar cututtuka

Majalisar dinkin duniya ta ce hare-haren da ake kai wa babu kakkautawa a birnin Aleppo na kasar Syria sun jefa kimanin mutum 2m cikin matsanacin halin rashin ruwan sha da yiwuwar kamuwa da cututtuka.

Hukumar kula da kananan yara ta majalisar dinkin duniya, Unicef ta ce hare-haren da aka rika kai wa ranar a Juma'a sun hana a gyara bututan da ke kai ruwa yankin da ke hannun 'yan tawaye na cikin birnin.

Unicef ta kara da cewa su ma 'yan tawayen sun toshe babban bututun da ke kai ruwa a yankunan da ke hannun gwamnati a birnin na Aleppo a wani mataki na ramuwar gayya.

An bayar da rahotannin kai sababbin hare-hare a birnin ranar Asabar, a yayin da dakarun sojin Syria ke matsawa domin sake kwace yankunan da ke hannun 'yan tawaye.

An kaddamar da sababbin hare-haren ne bayan yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla ta ruguje ranar Litinin.

Mataimakin shugaban Unicef Justin Forsyth ya shaida wa BBC cewa: "A hankali birnin Aleppo yana rugujewa, kuma dukkan duniya tana kallon abin da ke faruwa. An rufe hanyoyin da ruwa ke isa birnin sannan ana ta jefa bama bamai - hakan laifi ne na cin zarafin bil adama."