United ta casa Leicester 4-1

Shin United za ta iya daukar kofin Premier na bana?

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

United ta fara kakar wasan bana da kafar dama

Manchester United ta doke Leicester City, wacce ke rike da kambun gasar Premier da 4-1 a wasan da suka yi ranar Asabar.

Dan wasan United Chris Smalling ne ya fara zura kwallo yayin da Juan Mata ya bi sawunsa.

Marcus Rashford da Paul Pogba ma kowanne ya zura kwallo daya, inda Demarai Gray ya ci wa Leicester ta ta kwallon.

Jose Mourinho bai saka kyaftin din kungiyar Wayne Rooney sai a minti na 83.

Wannan ne karo na uku da ake doke Leicester a kakar wasa ta bana.