Karya ake yi da aka ce ba zan iya taka leda ba — Sakho

Sakho ya ce kalau yake

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Liverpool ta sayi Mamadou Sakho a shekarar 2013 daga Paris St-Germain kan £18m

Dan wasan baya na Liverpool Mamadou Sakho ya ce yana da koshin lafiyar da zai iya murza wa kungiyar leda.

Kwanakin baya ne dai kocin kungiyar Jurgen Klopp ya ce dan wasan, mai shekara 26, wanda bai buga wa kungiyar wasa ba tun a watan Aprilu, ba shi da karsashin da zai iya buga wasa.

Sai dai Sakho ya wallafa a shafinsa na sada zumunta cewa yana da azamar iya taka leda.

A cewarsa, "Na amince da halin da nake ciki, amma ba zan amince kan karyar da ake yadawa a kaina ba. Ya kamata magoya bayana sun san gaskiyar lamari. Yau mako uku ke nan tunda na samu karsashin yin kwallo."

A watan Mayu ne dai Uefa ta yi watsi da zargin da ake yi wa Sakho na amfani da kwayoyin kara kuzari.

Daga nan ne kuma aka ba shi umarnin zaman gida lokacin wasannin sada zumunta da Liverpool ta yi a Amurka a watan Yuli bayan sau uku yana yin jinkirin zuwa wajen atisaye.

Sakho ya yi zargin cewa kungiyar ba ta so ya buga mata wasa, kodayake "ban san dalilin hakan ba."