Zidane ya fadi dalilin da ya sa ya canza Ronaldo

Real Madrid
Bayanan hoto,

Wasanni biyu ne kadai Ronaldo bai buga wa Real Madrid ba a kakar bana

Kociyan Real Madrid, Zinedine Zidane, ya ce ya sauya Cristiano Ronaldo daga wasa ne saboda ya rika samun hutu.

Ronaldo bai ji dadi ba da aka sauya shi saura minti 18 a tashi wasan da Real Madrid ta buga 2-2 da Las Palmas a gasar La Liga a ranar Asabar.

Sai dai Zidane ya ce ya kamata Ronaldo ya amince da cewar wani lokaci dole ne a cire shi daga wasa.

Kocin ya kara da cewa ya san da cewar dan kwallon yana so ya buga wasanni sannan a dinga kammalawa da shi, to amma dole ne a rika sauya shi.

Kociyan ya ce dole ne ya rika tunanin kan 'yan wasansa da shi kansa, kuma dole ne a cire shi a wasan domin ya huta, domin tunkarar wasan kofin zakarun Turai ranar Talata.

Real Madrid, mai rike da kofin zakarun Turai, za ta ziyarci Borussia Dortmund a ranar Talata a wasa na biyu na cikin rukuni.