Hamilton na fatan samun nasara a Malaysian Grand Prix

Asalin hoton, Getty Images
Rabon Hamilton da ya lashe tsere tun a watan Yuli
Lewis Hamilton ya ce yana da kwarin gwiwar cewa zai farfado domin kare kanbunsa na gasar tseren motoci ta Formula 1 a karo na hudu.
Hamilton na mataki na biyu da tazarar maki takwas tsakaninsa da Nico Rosberg a daidai lokacin da ya rage wasanni shida a kammala gasar.
A ranar Lahadi ne za a fafata a gasar Malaysian Grand Prix.
Zakaran na duniya mai shekara 31 ya ce: "Akwai bukatar samun sakamako mai kyau domin lashe gasar.
Sai dai ya ce samu irin wadannan nasarori a baya, a don haka babu dalilin da zai sa ya fitar da rai a yanzu".
Abokin wasansa na tawagar Mercedes Nico Rosberg ne ya lashe wasanni uku a jere na baya, inda ya kawar da tazarar maki 19 da Hamilton ya bashi a karshen watan Yuli.
Babban Labari
Minti Daya Da BBC
Saurari, Minti daya da BBC Safe 20/01/2021, Tsawon lokaci 1,14
Minti Ɗaya da BBC na Safiyar 20/01/2021 wanda Sani Aliyu da Nabeela Mukhtar Uba su ka karanto.