Leicester City: Kasper Schmeichel zai dawo taka-leda

Mai tsaron gida na Leicester City Kasper Schmeichel

Asalin hoton, Getty Images

Mai tsaron gida na Leicester City Kasper Schmeichel zai iya dawowa taka-leda a wasan farko da kulob din zai yi a gida a gasar cin kofin zakarun Turai da FC Porto a ranar Talata.

Wasanni uku Schmeichel ya shafe bai yi buga ba tun lokacin da Foxes suka doke Club Brugge a wasan farko na rukunin G.

Dan wasan na Denmark bai buga wasa biyu ba saboda buguwar da ya yi, haka kuma babu shi a wasan da Manchester United ta lallasa su da ci 4-1 a ranar Asabar.

Dan wasan tsakiya na Faransa Nampalys Mendy ma ba zai buga wasan ba saboda raunin da ya samu a idan sahunsa.

"Wannan labari ne mai dadin ji ga magoya bayanmu," a cewar kociyan Leicester Claudio Ranieri.

"Da dama daga cikinsu sun zo Bruges domin su ji kida. Amma kuma [Ranar Talata] wasu da yawa za su ji shi sosai.

"Zai yi kyau sosai idan muka ci gaba da taka irin rawar ganin da muka fara, sannan mu samu nasara."