Real Madrid za ta ziyarci Dortmund a gasar zakarun Turai

Real Madrid

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Madrid ta yi canjaras a wasanni biyu a jere a gasar La Liga

Borussia Dortmund za ta karbi bakuncin Real Madrid a gasar cin kofin zakarun Turai a wasa na biyu a cikin rukuni na shida a ranar Talata.

Madrid mai rike da kofin bara ta ci Sporting 2-1 a wasan farko na cikin rukunin, yayin da Dortmund ta doke Legia 6-0.

Real Madrid da Borussia Dortmund sun hadu a gasar cin kofin zakarun Turai sau goma, inda Madrid ta ci wasanni hudu, Dortmund ta samu nasara a karawa uku suka yi canjaras sau uku.

A 2013/14 da suka fafata a gasar, Madrid cinye Dortmund ta yi da ci 3-0 a Spaniya, Dortmund kuwa 2-0 ta doke Madrid a Jamus.

A wasanni ukun baya da kungiyoyin biyu suka kara a Jamus, Dortmund ce ta lashe wasannin.

Madrid ta yi canjaras a wasanni biyu a jere a gasar La Liga, yayin da Dortmund ta doke Wolfsburg da ci 5-1 har gida a Bundeslia.

Haka kuma Sporting za ta kece raini da Legia Warszawa a wasa na biyu na cikin rukunin na shida a gasar ta zakarun Turai.