Shugaban bakin Afirka Akinwumi Adesina na ziyarar a Nigeria

Asalin hoton, Getty Images
Mista Adesina tsohon ministan aikin gona ne na Nigeria
Shugaban Bankin raya kasashen Afirka na AfDB, Akinwumi Adesina, ya fara ziyarar aiki ta kwana biyu a Nigeria.
Wannan ziyarar dai ita ce ziyara ta farko da yake kawowa kasar tun bayan da aka zabe shi a matsayin shugaban bankin a shekarar da ta gabata.
Manufar ziyarar ta shi dai, ita ce samun hadin kai a bangarori da dama, ciki har da yadda Najeriya za ta magance matsalolin tattalin arziki da take fuskanta a baya-bayan nan.
Mista Adesina, wanda tsohon ministan aikin gona ne na Najeriyar, zai gana da shugabanni da 'yan kasuwa masu zaman kansu kan tattalin arzikin kasar.
Ana kuma sa ran zai bayyana wasu matakai da tallafi da bankin zai bai wa kasar domin shawo kan matsalolin da take fuskanta.
A ranar Litinin ne dai ake sa ran Mista Adesina, zai gana da manena labarai a Abuja domin yin karin haske kan ziyarar ta sa.