Serge Aurier zai shafe wata biyu a kurkuku

Serge Aurier ya yi wa wani dan sanda gula

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

Serge Aurier dan wasan kwallon kafa na kasar Ivory Coast zai sha daurin shekara biyu

An yanke wa dan wasan kwallon kafa na kasar Ivory Coast, Serge Aurier, wanda ya ke buga wa kulob din Paris St-Germain wasa, hukuncin zama a gidan yari.

Serge Aurier dai zai shafe watanni biyu a gidan kaso bayan da ya yi wa wani dan sanda gula.

An kuma ci tarar dan wasan $674 a kan lamarin wanda ya faru a wani wurin holewa a Paris a watan Mayu.

A halin yanzu dai an saki Serge Aurier, har sai bayan daukaka kara, wanda hakan ke nufin zai iya buga wa Paris St-Germain din wasa a gasar Champions League a ranar Laraba.

An dai dakatar da dan wasan mai shekaru 23 a farkon wannan shekarar bayan ya yi kalaman batanci a kan kocin kulob din na PSG.