Fifa ta soke hukumar hana wariyar launin fatar da ta kafa

A shekarar 2013 aka kafa hukumar

Asalin hoton, FIFA

Bayanan hoto,

Fifa ta soke hukumar hana wariya da ta kafa a shekarar 2013 saboda ta kammala aikinta.

Hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, ta kare shawarar da ta yanke ta rusa Hukumar Hana Wariyar launin fatar da ta kafa, inda ta ce ta kammala aikinta.

An kafa hukumar hana wariyar ne a shekarar 2013 domin bunkasa shawarwari wajen magance matsalar wariyar launin fata.

Masu suka dai sun saka ayar tambaya a kan wargaza hukumar, inda suka ce wariyar abu ne da ke cigaba da faruwa.

Sai dai Sakatare Janar ta Fifa, Fatma Samoura ta ce "dama akwai aikin da aka bukata hukumar ta cimma kuma ta aiwatar da aikin sosai".

Tsohon mamba a hukumar Osau Obayiuwana ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa" ya kadu da jin labarin amma bai yi mamaki ba.

"Ina ganin akwai abubuwa da dama da ya kamata ace hukumar ta ci gaba da yi - ciki har da gasar cin kofin duniya ta 2018 da za a yi a Rasha".

Amma ya kara da cewa shugabannin Fifa sun yanke wata shawarar ta daban.