Kano: Kotu ta ce a goge Kwankwasiyya daga gine-ginen gwamnati

Kofar Nassarawa a Kano

Asalin hoton, others

Wata babbar kotu a Jihar Kano ta yanke hukuncin a goge duk wata inkiyar Kwankwasiyya daga jikin gine-ginen gwamnatin jihar, wacce tsohuwar gwamnatin jihar ta saka.

Kotun ta yi hukuncin ne a wata kara da Abdullahi Maraya Barkum da Hassan Sani Indabawa da Hamisu Danwawu suka shigar tun a shekarar 2012.

Kotun dai ta ce ba daidai ba ne a yi amfani da dukiyar al'umma wajen kamabama akidar wani mutum ko kungiya ba.

A karshen watan Agusta ne, majalisar dokokin Kano ta amince da kudurorin soke sunan Kwankwasiyya a jikin gine-ginen gwamnati da kuma sauya sunayen wasu rukunin gidaje uku masu alaka da akidun tsohuwar gwamnati ta Rabi'u Musa Kwankwaso.

Abdul Adamu, wanda shi ne Lauyan masu kara, ya ce sun yi farin ciki da wannan hukunci bayan fadi-tashi na tsawon shekara biyar.

Yayinda Haruna Muhammad Falali, wanda daya daga cikin bangare uku da aka yi kara, ya ce sun karbi hukuncin, kuma ba za su daukaka kara ba.

Tuni dai aka fara goge inkiyar ta Kwankwasiyya a jikin wasu ayyukan raya kasa da tsohuwar gwamnatin ta aiwatar.

Daya daga cikin jagororin Kwankwasiyya a Kano, Dr Yunusa Dan Gwani, ya shaida wa BBC cewa bai ga hukuncin ba, kuma kawo yanzu ba zai ce komai ba game da shi.