Ayatollah Khamenei ya gargadi Ahmadinejad: Kada ka yi takara

Tsohon shugaban kasar Iran, Mahmoud Ahmadinejad

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Mahmoud Ahmadinejad ya yi dan tsokaci a kan tsayawa takara a zaben badi

Jagoran addini na Iran, Ayatollah Khamene'i ya umarci tsohon shugaban kasar, Mahmoud Ahmadinejad, da kada ya yi takara a zaben da za a gudanar badi.

Jagoran addinin ya ce tsayawar Ahmadinejad takarar ba za ta amfane shi ba, kuma ba za ta amfani kasar ba; ana dai kallon wadannan kalaman tamkar an rushe duk wani yunkuri ne na shigar Mista Ahmadinejad takarar.

Mista Ahmadinejad dai mutum ne mai janyo cece-ku-ce, musamman gabannin zanga-zangar da aka yi bayan sake zaben sa da aka yi a shekarar 2009, amma kuma ana masa kallon zakaran da zai iya samar wa masu ra'ayin mazan jiya damar sake karbar mulkin kasar.

Mahmoud Ahmeadinejad dai bai fito ya bayyana aniyar sa na tsayawa takara ba, amma ya dan yi tsokaci a kai a wasu hirarrakin da ya yi a baya bayan nan.