Boko Haram: An kai hare-hare kusa da Chibok a jihar Borno

Mutane na tserewa daga kauyukan da aka kai harin
Bayanan hoto,

An kai harin ne kusa da garin Chibok

A Najeriya rahotanni daga jihar Borno a arewacin kasar na cewa an kai hare-hare a wasu kauyuka uku wadanda ke kusa da garin Chibok a ranar litinin.

An kai hare-haren ne a kauyukan, Kubiribo da bautari da kuma kuburumbulah da basu da nisa garin na Chibok.

Rahotanni sun ce maharan da ake kyautata tsammani 'yan kungiyar boko Haram ne sun kashe mutane takwas ciki har da shugaban daya daga cikin kauyukan.

Tuni dai mazauna kauyukan suka tsorata inda suka tsere daga garuruwan nasu.

Har kawo yanzu dai hukumomin kasar ba su yi karin bayani ba dangane da harin