An cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta tarihi a Colombia

Sa hannun zai kawo karshen yakin shekaru 50

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto,

An saka fararen kaya a wajen sa hannun, domin nuna zaman lafiya

Gwamnatin Colombia da kuma 'yan tawayen kungiyar FARC, sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya wadda za ta kawo karshen yakin da aka shafe shekaru fiye da hamsin ana yi.

Shugaba Santos ya yiwa yan tawayen maraba kan shiga tafarkin dimokradiyya.

Yace a yanzu Colombia za ta sama abar misali a wajen kasashen duniya da ke fama da rikice-rikice, kuma ake neman hanyar kawo karshensu.

An sanya hannun ne a wajen wani kasaitaccen biki da aka gudanar a birnin Cartagena, wanda ya samu halartar manyan baki sama da 2,500 daga ciki da wajen Colombia .

Daga cikin wadanda suka halarci taron har da sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya da kuma shugabannin kasashen kudancin Amurka.

Da ya ke magana a wajen bikin sa hannun jagoran 'yan tawayen kungiyar ta Farc Timoliyan Himenes wadna aka fi sani Timoshonco ya nemi gafarar duk wadanda yakin ya shafa, kuma hakan ya sa an yi masa tafin jinjina.

"Ina neman gafarar duk wanda wannan wannan rikicin ya shafa, ina neman afuwar bisa duk wani rashin dadi da aka shiga lokacin yakin".

Timochenko yace kungiyar da aka kafa a matsayin wani bangare na jam'iyyar gurguzu a 1964, a yanzu za ta zubar da makamai ta shiga gwagwarmayar neman mulki ta hanyar dimkoradiyya.

Shugaban Colombia da kuma shugaban 'yan tawayen sun yi amfani da alkalamin da aka yi da albarushi wajen sanya hannun, wanda hakan ke nuna cewa an bar amfani da bindiga an koma amfani da ilimi a kasar ta Colombia.

Kimanin mutane 26,000 ne aka kashe a yakin basasar na shekaru 52, sannan mutane miliyan shida suka rasa gidajensu.

A karkashin yarjejeniyar dai kungiyar ta FARC za ta rikide zuwa jam'iyyar siyasa, to amma fa duka wannan zai kasance ne bayan kuri'ar jin ra'ayin jama'a da za a gudandar ranar 2 ga watan Oktoba.

Wasu 'yan kasar ta Colombia na takaicin cewa za a kyale 'yan tawaye suka shiga majalisar kasa, maimakon tsare su a gidan kaso.

A karkashin yarjejeniyar dai dole ne kungiyar ta Farc ta mikawa MDD makamanta cikin kwanaki 180.