Heather Watson 'yar wasan Birtaniya ta fice daga gasar Wuhan Open

Watson ta fice daga gasar Wuhan Open

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Heather Watson 'yar wasan Birtaniya ta fice daga gasar Wuhan Open

Heather Watson 'yar wasan Birtaniya ta fice daga gasar kwallon tennis ta Wuhan Open, sakamakon rashin lafiya.

Watson wadda ya kamata ta fafata da Madison Brengle ta Amurka a wasan zagayen farko, ta ce ba za ta iya wasan ba domin bata jin kwarin jikinka

Ita kuwa Johanna Konta ta kai wasan zagaye na biyu, bayan da ta doke Annika Beck ta Jamus da ci 6-1 da kuma 6-2 a cikin ruwan sanyi.

Konta, za ta kece raini tsakaninta da Zhang Shuai a wasan zagaye na biyu a gasar kwallon tennis ta Wuhan Open.