Nigeria: Za a binciki MTN kan biliyoyin daloli

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya yana jawabi a gaban Majalisar Dokokin Najeriya

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Majalisar dokokin Najeriya za ta binciki MTN

A ranar Talata ne 'yan Majalisar Dattawa a Najeriya suka amince a gudanar da bincike a kan zargin cewa kamfanin sadarwa na MTN ya fitar da kudin da yawansu ya kai dala biliyan 13.92 daga kasar ta haramtaciyyar hanya.

Sai dai zuwa yanzu kamfanin na MTN ya ki cewa komai a kan wannan shawara da majalisar ta yanke.

Mutane miliyan 62 ne dai ke amfani da layukan MTN a Najeriya, lamarin da ya sa kasar ta zama kasuwarsa mafi girma a Afirka.

Zuwa bayan sallar azahar a ranar Talatar dai darajar hannayen jarin kamfanin ta yi kasa da sama da kashi hudu cikin dari.

Ba dai wannan ne karon farko da kamfanin MTN ke takun-saka da hukumomin Najeriya ba.

A watan Oktoban bara ma, hukumar da ke sanya ido a kan kamfanonin sadarwa, NCC, ta ci tarar kamfanin dala biliyan biyar saboda ya ki rufe layukan mutanen da ba su yi rijista ba har wa'adin da aka diba domin yin rijistar ya wuce.

Sai dai daga baya hukumar NCC din ta rage tarar zuwa dala biliyan uku da miliyan dari hudu.