Mali: Ahmad al-Faqi zai sha daurin shekara tara

Asalin hoton, EPA
Ahmad al-Faqi ya yi nadamar abin da ya aikata
Kotun hukunta manya laifuka ta duniya, ICC, ta yanke wa dan tawayen kasar Mali, Ahmad al-Faqi al-Mahdi daurin shekara tara saboda rusa wuraren tarihi a Timbuktu.
Ahmad ya amsa cewa shi ne ya jagoranci sojojin 'yan tawayen wadanda suka lalata makabartu masu cike da tarihi a shekarar 2012.
Alkalai a kotun sun gano cewar ya yi nadamar aikata laifin.
Wannan ne hukunci na farko a kan barnar da ta shafi al'adu da kayan tarihi da kotun ta yanke a matsayin laifin yaki.
Kuma wannan ne karo na farko da kotun ta yi shari'ar wani mai tsattsauran ra'ayi.