Nigeria: Boko Haram ba su kafa tuta a Borno ba - sojoji

Boko Haram

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Sojoji sun fatattaki Boko Haram daga mafi yawan garuruwan da ta kama

Rundunar sojin Nigeria ta ce babu wata tutar Boko Haram da aka kafa a kauyuka ukun da 'yan kungiyar suka kai wa hari a jihar Borno.

Mazauna kauyukan Kubirivour, Boftari and Kuburmbalah da ke kusa da garin Chibok, sun shaida wa BBC cewa mayakan sun yanka mutane takwas, ciki har da wani dagaci.

Hakazalika wata majiyar tsaro da ta fararan hula ta shaida wa BBC cewa mayakan Boko Haram sun kafa tutocinsu a .

Sai dai mai magana da yawun rundunar sojin Kanar Sani Usman ya ce babu wanda aka kashe, sannan ya musanta rahotannin cewa Boko Haram ta kafa tutarta a kauyukan.

Kanar Usman ya ce mayakan sun kona wasu gidaje kafin sojoji su fatattake su.

Ya kara da cewa wani dan kato-da-gora guda kawai aka jiwa rauni, yayin da 'yan bidigar da dama suka tsere da raunuka a jikinsu.

Rahotanni sun ce akalla mutane 17 ne aka jikkata a hare-haren na ranar Litinin.

Wata majiya ta ce har yanzu mayakan Boko Haram na rike da garin Malam Fatori, wanda ke kan iyakar Najeriya da Nijar.

A makon da ya gabata ne sojojin Najeriya suka kwato garin daga hannun mayakan Boko Haram.

Sai dai rahotanni sun ce 'yan bindigar sun sake damara inda suka sake kwace iko da garin.

Wakilin BBC a Najeriya ya ce hare-haren na baya-bayan nan na nuna yadda har yanzu kungiyar ta Boko Haram ke ci gaba da zama barazana ga kasar.