Nigeria: Majalisar wakilai ta dakatar da Abdulmumini Jibrin

Hon Abdulmumini Jibrin
Bayanan hoto,

Hon Abdulmumini Jibrin ya musanta zargin da aka yi masa

Majalisar Wakilan Nigeria ta dakatar da tsohon shugaban kwamitin kasafin kudinta, Abdulmumini Jibrin, na tsawon watanni shida, bayan da ta same shi da laifin karya ka'idojinta.

Dan majalisar, wanda ke wakiltar Kiru da Bebeji a Kano, ya shiga takun-saka da shugabannin majalisar ne bayan da ya zarge su da yin cushe a kasafin kudin kasar na shekarar 2016.

An kuma haramta masa rike kowanne irin mukami a majalisar har zuwa karshen wa'adin wannan majalisar - wato 2019.

Kazalika sai Jibrin ya rubuta takardar neman afuwa tukunna kafin ya dawo zauren majalisar, ko da wa'adin dakatarwar ya cika.

Kwamitin da'a na majalisar ne ya bayar da rahoton binciken da ya yi kan zargin bata sunan majalisa da kuma saba ka'idojinta, wanda mafi yawan 'yan majalisar suka amince da shi.

Sai dai Honourable Jibrin bai halarci zaman ba, yana mai cewa ba za a yi masa adalci ba.

Ya kara da cewa lamarin na gaban shari'a.

'Abin da ya jawo rikicin'

Yakubu Dogara
Bayanan hoto,

A baya Yakubu Dogara yana dasawa da Abdulmumini Jibrin

A watan Yuni ne dai Honourable Jibrin ya yi zargin cewa Shugaban Majalisar Yakubu Dogara da wasu manyan 'yan majalisar sun yi yunkurin yin aringizon N30bn a kasafin kudin shekarar 2016.

Dan majalisar, wanda aka sauke daga shugabancin kwamitin da ke kula da kasafin kudi, ya ce an sauke shi ne saboda yana adawa da shirin kafa dokar da za ta bada rigar-kariya ga shugabannin majalisar wakilan da ta dattawa.

Mista Jibrin ya kara da cewa "Ina da shaidun da ke nuna cewa Dogara, da mataimakinsa Yusuf Lasun, da Alhassan Doguwa da Leo Ogor sun ware wa kansu 40bn a cikin 100bn da aka warewa gaba dayan majalisar dokokin tarayya ta Najeriya.

Sai dai mai magana da yawun majalisar wakilan, Abdulrazak Namdas, ya musanta zarge-zargen da Mista Jibrin ya yi, yana mai cewa zafin cire shi da aka yi daga shugabancin kwamitin kasafin kudi ne ke damunsa.