Leicester City ta ci Porto a gasar zakarun Turai

Islam Slimani ne ya ci wa Leicter kwallon

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto,

Leicester City ta doke FC Porto

Leicester City ta doke FC Porto da ci daya mai ban haushi a gasar cin kofin zakaru da suka fafata a ranar Talata.

Islam Slimani ne ya ci wa Leicester kwallon, bayan da ya samu tamaula daga bugun da Riyad Mahrez ya yi masa.

Wannan shi ne wasa na biyu da Leicester ta lashe a gasar ta cin kofin zakarun Turai, bayan da ta doke Club Brugge a wasan farko na cikin rukuni.

Da wannan sakamakon Leicester ce ke kan gaba a kan teburin rukuni na bakwai da maki shida, sai FC Copenhagen a matsayi na biyu.

Ga sakamakon sauran wasannin da aka buga a ranar Talata:

Monaco 1 : 1 Bayer Leverkusen

CSKA Moscow 0 : 1 Tottenham

Borussia Dortmund 2 : 2 Real Madrid

Sporting 2 : 0 Legia Warszawa

Sevilla 1 : 0 Lyon

Dinamo Zagreb0 : 4 Juventus

FC Copenhagen 4 : 0 Club Bruges

Leicester 1 : 0 FC Porto