Arsenal za ta ziyarci Basel ba tare da Coquelin ba

Asalin hoton, Rex Features
Arsenal za ta taka leda ba tare da Francis Coquelin
Arsenal za ta kara da Basel a gasar cin kofin zakarun Turai wasa na biyu na cikin rukuni farko a ranar Laraba, ba tare da Francis Coquelin ba sakamakon raunin da ya yi.
Dan kwallon mai buga wasan tsakiya ya yi rauni ne a gwiwarsa a karawar da Arsenal ta ci Chelsea 3-0 a gasar Premier a ranar Asabar.
Arsene Wenger ya ce yana fargabar raunin da dan kwallon ya yi, domin iri daya ne da wanda ya yi a bara wanda ya sa ya yi jinyar wata biyu.
Shi ma Olivier Giroud ba zai buga karawar ba, sakamakon jan kati da aka bashi a wasan farko da Arsenal ta buga kunnen doki 1-1 da Paris St-Germain a Faransa.