Ingila da Allardyce sun raba gari

Ya bar matsayin kocin ne sabo da an gano ya aikata ba dai-dai ba

Asalin hoton, LNP

Bayanan hoto,

Wasa daya kawai Sam Allardyce ya jagoranci Ingila

Hukumar kwallon kafa ta Ingila da Sam Allardyce sun raba gari, bayan da kociyan ya jagoranci tawagar kwallon kafar kasar wasa daya kacal.

Raba garin da suka yi ya biyo bayan binciken da wata jarida ta gudanar, wadda ta ce Allardyce ya bayar da shawara kan yadda za a karya ka'idar sayen dan kwallo.

Jaridar ta kuma zargi kociyan mai shekara 61 da yin amfani da mukaminsa, inda ya shiga yarjejeniya ta kudi fam 400,000 domin ya wakilci wani kamfani.

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta ce abinda Allardyce ya aikata bai dace ba, ta kuma nada Gareth Southgate a matsayin kociyan rikon kwarya.

Allardyce wanda ya yi kwanaki 67 a matakin kociyan tawagar kwallon kafa ta Ingila, ya maye gurbin Roy Hodgson ne a cikin watan Yuli.