Nigeria: Majalisar wakilai za ta karbi rahoto kan zargin cushe a kasafi

Abdulmumini Jibil ya ki zuwa gaban kwamitin
Bayanan hoto,

Za a mikawa majalisa rahoto kan Abdulmumini

A Najeriya, a ranar Larabar nan ne ake sa ran kwamitin da`ar majalisar wakilan kasar zai mika rahotonsa game da zaman da ya yi don jin bahasi daga tsohon shugaban kwamaitin kasafin kudin majalisar, Hon Abdulmumini Jibril, wanda ya zargi shugabannin majalisar da yin cushe a cikin kasafin kudin kasar.

Hon. Abdulmumini Jibril dai bai halarci zaman kwamitin ba.

Majalisar wakilan na zargin dan majalisar da bata wa shugabanninta suna da kuma saba wa ka`idojinta, kuma wata majiya ta tabbatar wa BBC cewa watakila a yanke masa hukuncin dakatarwa daga majalisar ta tsawon wata shida, idan an same shi da laifi.

Hon. Abdurrazak Namdas shi ne shugaban kwamitin watsa labaran majalisar, ya ce tun da an bawa Abdulmumini damar kare kansa amma bai je ba, to ko wane mataki majalisar ta dauka ba shi da kaico.

To amma a bangare guda kuma, tsohon shugaban kwamitin na kasafin kudi Hon Abdulmumini Jibril ya ce ya ki zuwa gaban kwamitin ne, sabo da ya gano cewa kwamitin ya dauki bangare.