Shahararren dan siyasar Isra'ila Shimon Peres ya mutu

Shi ne na karshe a cikin mutanen da aka kafa Israela da su

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto,

Shimon Peres ya mutu yana da shekaru 93

Shahararren dattijon dan siyasar nan na Isra'ila Shimon Peres ya mutu yana da shekara 93.

Makonni biyu da suka wuce ne aka kwantar da shi a asibiti saboda shanyewar barin jiki.

Da farko dai ya dan samu sauki amma sai kwatsam jikin na sa ya kara rikicewa a jiya Talata.

Shimon Peres -- wanda shi ne mutum na karshe daga wadanda aka kafa Isra'ila da su -- ya yi aiki a gwamnatoci 12, ya zama firayi minista sau biyu, sannan ya taba zama shugaban Isra'ila.

A farkon rayuwar Shimon Peres dai ana yi masa kallon dan ina-da-yaki, amma a shekarun 1990 ya taka muhimmiyar rawa wajen cimma yarjejejniyar zaman lafiya da Falasdinawa, saboda haka ne ma ya samu lambar yabo ta Nobel, tare da Yitzhak Rabin na Israi'la da Yaseer Arafat na Palasdinu.

Ya taba cewa Palasdinawa sune makota na kusa ga Isra'ila, kuma za su iya zama abokai mafiya kusanci.

'Duniya na alhini'

Dansa Chemi ya bayyana da cewa "yana daya daga cikin mutanen da suka kafa tushen Isra'ila" wanda "ya yi aiki tukuru" domin ganin wanzuwarta.

Firai Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya bayyana "matukar juyayi" a kan mutuwar Mr Peres.

A wata sanarwa da ya fitar ta bidiyo ya bayyana shi a matsayin "Mutum mai hangen nesa."

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayyana Mr Peres a matsyin "babban abokina" a wata sanarwa da ya fitar, yana mai karawa da cewa: "Yana da tausayin dan adam da son ci gaba."

An sa ran shugabannin duniya da dama za su halarci jana'izarsa wacce za a yi a birnin Qudus ranar Juma'a, cikinsu har da shugaban Amurka Barack Obama, da Yarima Charles na Birtaniya da kuma Pararoma Francis.