MTN ya musanta zargin janye $13.92 bn daga Nigeria ba bisa ka'ida ba

Asalin hoton, Getty Images
MTN Ya ce zargin ba shi da tushe
Kamfanin sadarwa na MTN ya musanta zargin da aka yi masa cewa ya janye $13.92 bn daga Najeriya ba bisa ka'ida ba.
Wata sanarwa da shugaban kamfanin a Najeriya Ferdi Moolman ya fitar ranar Laraba ta ce "zargin ba shi da tushe bare makama."
A ranar Talata ne dai majalisar dattawan kasar ta umarci a yi bincike kan zargin.
Idan har ta tabbata cewa kamfanin ya janye kudin daga Najeriya, hakan zai iya shafar tattalin arzikin kasar wanda ke cikin mawuyacin hali sakamakon karancin kudaden waje da hauhawar farashi.
A kwanakin baya ne dai MTN ya amince ya biya Najeriya tarar N330bn bayan an same shi da lafin kin yanke layukan wayoyin miliyoyin mutane, inda ake zargi ana amfani da su wajen aikata ta'addanci.